Monday, September 15, 2008

SADUWA DA MATA CIKIN HAILA

SADUWA DA MATA CIKIN HAILA


Allah Madaukakin Sarki Yace:
( Kuma Suna tanbayarka game da Haila , Kace kazanta ne , Ku Nisanci Mata a cikin Haila , kuma jada ku kusance su har se sunyi tsarki)[Suratul Baqarah - 222].
Saboda haka baya halatta wato Haramun ne Mutum ya kusanci matarsa har se tayi wanka bayan tsarki ,
saboda Fadin Allah Madaukakin Sarki:
(To idan Sunyi tsarki Se kuzo masu ta inda Allah Ya Umarce ku…) [Suratul Baqarah - 222]. Kuma abinda ke nuna munin wannan Laifi Shine Hadisin da Abu Hurairah Yace: Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yace: (Duk Wanda yazo ma me Haila , ko yazo ma mace ta bayanta , ko yaje wajen Boka , to ya kafirta daga abinda aka Saukar wa Muhammad) [ Imamu Tirmidhi-Vol.1- 243].
Ma’ana wanda ya sadu da matarsa alhali tana cikin Haila , ko ya sadu da ita ta wurin bayan gidanta. To duk wanda ya aikata hakan da kus – kure , bada gan – gan ba , alhali be sani ba , babu komai akansa , wanda kuma ya aikata hakan dagan - ganci yana sane , To zeyi kaffara a daya daga cikin zantukan Malamai wanda sukace hadisin kaffara ya inganta , shine yayi sadaka da Dinar wato Zinare ko rabin Zinare , Wasu sukace yanada zabi cikinsu wato kodai ya bada Zinare ko rabinsa , Wasu Malaman Sukace: Idan yazo mata a lokacin da ta fara Haila to ze bada Zinare cikakke , idan kuma a karshen Hailan yazo mata wato lokacin da jinin ya ragu ko kafin tayi wankan Haila to ze bayar da rabin Zinare. Zinare cikakke kuma ana kwatantashi da 4.25gram ko da kudin da ake sayar dashi. Sannan abinda Malamai sukace shine dai – dai shine Zance da’akace yanada zabi tsakanin zinare ko rabinsa

Saturday, July 5, 2008

SHIN KE MACE ME KOKARI NE?

Abune dayake sananne cewa kina fuskantar matsaloli cikin ranki da kuma zamantakewa a wajen kulla Alaka da aikace - aikacenki, to abinda yakamata kisani shine rayuwa bata rabuwa da wadannan matsalolin, kuma babu shakka nasan cewa sau dayawa kin yi tunani akan wata matsala da ta faru dake, bayan kin dauka mataki domin kiga shin kinyi dai dai koko shin kin yi kuskure? akan matakin dakika dauka, daganan kina kara samun kwarewa wajen magance matsalolinki, ba’a baukatan koda yaushe kizama me ran karfe wajen war - ware matsaloli, amma ga wasu abubuwa dazasu temaka maki wajen hakan

  1. Kiyi abinda ake kira jeranta abubuwa gwargwadon muhimmancin su wato (First thing First) kuma ki tsara ayyukanki,, hakan ze kareki daga damuwa, saboda kina zartar da abinda yakeda muhimmanci sosai, kuma ze rage maki damuwa, saboda ayyukan da bakiyi su ba, basu da muhimmanci sosai.
  2. Kada ki dora ma kanki abinda yafi karfinki, Allah Madaukakin Sarki yace: (La yukallifullahu nafsan illa wus aha Suratul Bakara 286. Ma'ana Allah baya kallafa ma rai face abinda take iyawa. To ya tausaya mana saboda haka yakamata mu tausaya ma kawunanmu, amma batare da kasala ba ko rashin yin aiki, kuma kada kice se kinyi komai da kikeso, wato ki cika komai, domin cika na Allah ne kadai, takenki yazama “Adai daita sahu”
  3. Kada ki shagaltu da aiki fiye da daya, a lokaci guda domin ze kasa hankalinki biyu da kokarin dakikeyi, daga nan baza ki iya yin aiki kwakkwara ba me aminci, abinda yakamata shine: ki kammala wani sannan ki fara nagaba dashi, domin hakan ze saki jin dadi da jin cewa kina samun nasara a rayuwa, kuma ze sa kiyi kwadayin aiwatar da wani aikin.
  4. Wajen alakar ki da sauran jama’a kuma: kiyi kokari ki fuskance su da rashin yin karya kuma bada barin gaskiya ba, A’a cikin natsuwa da hankali, kuma kada kiyi fushi, idan wasu basuyi kawance dake ba, haka kuma ki karbi kuskure idan anyi maki gyara, sawa’un daga kawayenki ne ko wasu daban, ki dauki hakan a matsayin jarrabawa na fadada kirjin ki (wato koyan yin hakuri).
  5. kada kibar jarabawa da baki samu nasara ba akanta, ta hana ki aiwatar da wani aiki, yin tunani akan abinda baki samu nasara ba akansa zesa kiyi wanda yafishi kyau, abinda ya kamata ki dauki rashin samun nasaranki a matsayin ma’auni na samun darasi da kwarewa. Ba matsayin tsoro ba.
  6. Wajen alakanki da sauran jama’a, ki dinga kokarin yawan mur mushi, kuma ki tuna da hadisin da ke cewa “ Yin mur mushin ka ga dan uwanka SADAKA ne" – (wato akwai lada a cikinsa) kuma ki sani dariya na kara maki soyayya dake sa zuciya ta natsu, kuma kiyi kokarin yin Magana da sauti dan kadan domin daga sauti na kara rashin jituwa.
  7. Likitoci suna cewa: Cakuda jiki yana temakawa wajen rage rashin natsuwa da damuwa, To saboda haka ki kwatanta kigani, musamman wajen wanka, da lokacin alwala ki dinga caccakuda yatsun hannu da na kafa.
  8. Ki yi kokari ki dinga yin Zikirin Safiya da na Marece, ze saki a koda yaushe kizama kina tareda Allah, kuma ze kara maki jin cewa Allah yana ganinki a koda yaushe, kuma kina cikin Kariyarsa, kuma kina da ikon ketare kowani abu dayake da wahala, da war - ware matsaloli da datarwansa (ikonsa), ki rokeshi dacewa, da yin dai - dai, Shi Allah yana yaye bakin ciki, kuma yana amsan rokon wanda ya kirasa (mabukaci).
  9. Kada ayyuka ko damuwa susa ki dinga jinkirta sallah, SALLAH hutu ce ga rai kuma natsuwa ce ga zuciya, Kuma Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya kasance yana cewa “Bilal ka hutar damu da Sallah” lokacin da zece ya tada ikama.
  10. Kada kiyi kokarin Boye rashin jin dadinki da damuwanki, A’a kiyarda cewa kinada damuwa, amma ki amince cewa kina da ikon da zakiyi nasara akansa, kuma idan kikaji cewa kinaso kiyi kuka, to kada kiyi kokwanto kiyi kuka da hawaye domin yin kuka ba dalili ne na rashin iko ba ko shi ke nuna kina da rauni, a’a kuka hanya ne na rage damuwa da rai ke ciki.

Saturday, June 21, 2008

SHAWAR-WARI GA MACE ME CIKI

Bismillahir Rahmanir Rahim

Y'ar Uwa a musulunci: wadannan wasu shawar-wari ne da likitoci suke baiwa Mace me goyon ciki, da fatan zaki kula da su da kyau.

1. Ki baiwa abinda ke cikin ki kula matuka, saboda kisami lafiya da kubuta, ke da abinda ke cikinki insha Allahu.

2. Yakmata ki dinga cin abinci sosai, irin wanda yake gina jiki, ta yanda zaki sami lafiya, da d'an dake ciki.

3. Ki dinga cin kayan mar-mari, kaman su kwad'on rama ko latas da makamantansu a kowace rana.

4. Ki dinga shan kaman kofi hudu na madara, ko nono a kowace rana.

5. Kada ki dinga yawan Shan Shayi mara madara, ko Nescafe, ko cin albasa, ko cin yaji a abinci, domin ha………

6. Kada ki dinga shan magani, ba tare da shawartan likita ba, saboda hakan ze cutar da yaron, kai yana temakawa wajensa Yaron Muni.

7. Yanada kyau a rage saduwa da Iyali, lokacin da cikin yake wata uku, da kuma watan karshe na haihuwa, yawan aikata hakan yana tasiri ga lafiyarki da ta Yaron.

Sannan saduwa da mace lokacin da take cikin jinin haihuwa yanada cutarwa ga mace, saboda hakane musulunci ya haramtashi.

8. Rashin yin barci da wuri, ze sanya maki damuwa, saboda haka dolene kiyi barci na Awa tara a kowace rana, a tsawon lokacin goyon cikin.

9. Kada ki dinga yin aiki me wahala da d'aga abubuwa masu nauyi, domin hakan ze Iya samar da matsala ga cikin.

10. Ki lazimci Natsuwa, da rashin yin fushi, sakamakon wasu matsaloli na gida, ko na Y'an Uwa, saboda ki samu kwanciyan hankali, ana buk'atan hakan dan cikin yatafi yanda akeso, batare da wata matsala ba.

11. Kada ki dinga ziyartan marasa lafiya, masu dauke da ciwon daza'a iya kamuwa dashi, don ze zama hatsari agareki da kuma danki.

12. Kada ki dinga sanya tufafi masu matse jiki, ko daure ciki da k'arfi tsawon lokacin goyon cikin, dan yin hakan ze saki gajiya, da shan wahala wajen yin numfashi.

13. Kada ki dinga sanya takalma masu tsawo, wato masu dogon k'wauri dan ze sabbaba rashin walawa a gab'ubb'an jikinki, wanda hakan ze samaki ciwon baya.

14. Dolene ki dinga yawan ziyartan likita akai-akai, tsawon lokacin goyon cikin, Sau d'aya cikin kowani wata cikin wata shida na farko, da kuma sau d'aya cikin kowani sati biyu, a watana bakwai da na takwas, da kuma sau daya cikin kowani sati, a watana tara har zuwa lokacin haihuwa.

15. Ki dinga yin gwajin jini da na fitsari, lokaci zuwa lokaci saboda ki tabbatar cewa: jikinki baya dauke da wani ciwo da yaron ze iya kamuwa dashi, kaman ciwon sukari da makamantansu.

16. Dolene ki dinga yin wanka a kowace rana, a duk lokacin tsawon goyon ciki, da lokacin shayarwa, dan ki kare lafiyarki, da na yaronki. Insha Allahu.

17. Ki dinga kula da mamanki, tun daga wata na biyar da samun cikin, saboda shayar da danki mama na asali.

18. Ki dinga tafiya da k'afa a kowace rana, gwargwadon iyawarki, hakan ze kyautata maki jinin jiki lokaci zuwa lokaci, ya zama abinci ga danki, kuma ya sauwak'e maki haihuwa.

19. Anason haihuwa a asibiti, saboda samun kula da Uwa da danta, kuma babu laifi ta haihu a gida idan ta shawarci kikita ya tabbatar mata da cewa duk abinda ya shafeta da d'anta yana tafiya daidai, kuma ya nisantarda samun wata matsala, kuma yazama akwai abubuwan da suka shafi samun lafiya a gida.

20. Ki dinga yin ayyukan gida, ke da kanki bayan kin haihu da y'an kwana kadan, domin hakan zesa mahaifarki ta koma yanda take ada, ya karfafa maki gab'ob'in jiki, kuma ya hana …..ciki da k'irji, kuma ya temaka wajen samar da mama ga jariri.

Allah nake roko da ya sauwak'e maki wahalhalun haihuwa kuma ya baki zurriyya ta k'warai Allahumma Amin.